‘Ƴan Najeriya za su yi kewar Buhari idan ya sauka daga mulki – Garba Shehu

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Babban mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan kafafen yaɗa labarai, Mallam Garba Shehu ya koka kan irin caccakar da ake yi wa shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari.

 

Ya ce ba a nuna ƙauna ga shugabanni a lokacin da suke mulki.

 

Saudiyya ta gargaɗi masu ɗaukar hoto a lokacin ziyarar ibada

Ya bayar da misali da zamanin mulkin Goodluck Jonathan wanda ya ce mutane sun yi ta sukarsa amma a yanzu, ya zama mutumin da ƴan Najeriya da dama ke yabo.

INEC ta saka ranar ƙarasa zaɓukan da ba a kammala ba

 

Mallam Garba Shehu ya ce irin haka za ta faru idan Buhari ya miƙa mulki ga shugaban ƙasa na gaba.

 

Game da manufar taƙaita amfani da garin kuɗi, Garba Shehu ya ce tsarin na gwamnati mai ci abin so ne a don haka ba za a soke shi ba.

 

A cewarsa, “taƙaita amfani da takardun kuɗi ci gaba ne ga ƴan Najeriya saboda ƙasashen da suka ci gaba tuni suke tafiya a kan wannan tsarin”.

 

Al’ummar Najeriya sun yi ta fuskantar matsaloli saboda ƙaranvin takardun kuɗi tun bayan da gwamnati ta bijiro datsarin sauya fasalin takardun kuɗin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...