Daga Kamal Yahaya Zakaria
Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC reshen jihar kano zata baiwa zaɓaɓɓen gwamnan jihar kano Injiniya Abba Kabir Yusuf shaidar lashe zabe a ranar laraba mai zuwa.
Mai magana da yawun sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, wato Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fidda sanarwar cewa, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta shirya mika takardar shaidar nasarar lashe zaɓen gwamna ga Abba, da kuma mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
INEC ta saka ranakun bai wa zaɓaɓɓun gwamnoni takardar shaidar cin zaɓe
Sanarwar ta kara da cewa, taron zai gudana ne a ranar Laraba 29 ga watan da muke ciki na Maris, wanda hukumar zata hada tare da zaɓaɓɓun yan majalisar dokokin jihar Kano wajen basu Satifket din.
Za a fara ƙidaya a ranar 3 ga watan Mayu — Gwamnatin Tarayya
An samu kace-nace tsakanin magoya bayan jam’iyyar NNPP da kuma APC a jihar Kano, musamman yadda APC tayi zanga-zanga da kiran INEC ta sake bibiyar sakamakon zaɓen domin mayar dashi wanda bai kammala ba, wato Inkwankulusib.