Sarkin Bichi ya taya Abba Gida-gida Murnar lashe zaɓen gwamnan Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya taya zababben Gwamnan Jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf murnar lashe zaben gwamnan jihar,wanda aka gudanar a ranar asabar 18 ga watan maris na 2023.
Alhaji Nasiru Ado Bayero ya bayyana murnar ta shi ce cikin wata wasika ta taya murna da ya aikawa zababben gwamnan, wanda wasu daga cikin hakiman Masarautar suka kaiwa zaɓaɓɓen gwamnan.
Mai martaba Sarkin na Bichi ya taya Abba Gida-gida da mataimakin sa Kwamarat Aminu Abdulsalam murna tare da fatan zasu gudanar da mulkin da zai kawo wa jihar kano cigaba ta fuskar inganta Ilimi tattalin arziki da Samar da aiyukan raya kasa da cigaban al’umma.
” Muna baku tabbacin masarautar Bichi zata baku cikakken hadin kai da goyon baya don ku Sami damar gudanar da aiyukan cigaba a jihar Kano baki daya, muna addu’ar Allah ya taya ku riko ya baku damar hidimtawa al’ummar jihar kano”. Inji Sarkin Bichi
Tawagar mai martaba Sarkin ta ziyarci zaɓaɓɓen mataimakin gwamnan Kano ƙarshin jagorancin Madakin Bichi Alhaji Nura Shehu Ahmad.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Sauran masautun Kano sun mikawa Abba Gida-gida sakon taya shi murnar lashe zaben gwamnan jihar kano da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta baiyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar asabar 18 ga watan maris na 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku ba da gudunmawa kano ta zauna Lafiya – Waiya ya shawarci yan jaridun yanar gizo

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci kafafen yada labarai na...

KAROTA ta tabbatar da aniyarta na inganta matsayin jami’anta

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano...

Sarkin Sanusi ya amince da nadin sabon mai unguwar Hotoro GRA

  Mai martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi...