INEC ta yi dai-dai da ta ayyana zaben gwamnan Adamawa a matsayin wanda bai kammala ba – Binani

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

‘Yar takarar kujerar gwaman jihar Adamawa ƙarƙashin jam’iyyar APC Sanata Aishatu Ahmed Binani, ta bayyana goyon bayanta kan matakin hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka na bayyana zaɓen gwaman jihar a matsayin wanda bai kammala ba.

Yayin da ta bayyana a cikin shirin ‘Politics Today’ na gidan talbijin ɗin Channels Tv, Sanata Aishatu Binani ta yi maraba da matakin, inda ta yi zargin cewa an aikata kura-kurai da rikice-rikice a wasu ƙananan hukumomin jihar.

Akwai gwamnoni da Ministocin za mu tuhuma bayan May 29

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar Farfesa Muhammadu Mele na jami’ar Maiduguri ne ya ayyana sakamakon zaɓen gwaman jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.

Sarkin Bichi ya kaddamar da sabuwar tashar wutar lantarki da Masarautar ta samar don inganta rayuwar al’umma

Gwaman jihar mai ci Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ke neman wa’adin mulkin jihar karo na biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 421,524, yayin da ita kuma Sanata Binani ta jam’iyyar APC ke da yawan ƙuri’u 390,275.

Jami’in zaɓen ya bayyana cewa ba a gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe 69 a faɗin jihar ba, kuma adadin katunan zaɓen da aka karɓa a duka rumfunan sun kai 37,016, wanda kuma adadinsu ya zarta tazarar ƙuri’u 31,249 da ke tsakanin ‘yan takarar biyu.

Sanata Aishatu ta ce ”matsayina game da matakin shi ne jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar ya yi daidai da ya bayyana sakamakon zaɓen jihar a matsayin wanda bai kammala ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...