Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya amince da shan kaye a zaben gwamna da aka kammala a jihar.
Matawalle ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Dauda Lawal Dare.
Gawuna ya taya al’ummar musulmi shigowa watan Ramadan
A wani sakon murya da ya aikewa al’ummar jihar, Gwamna Matawalle ya ce dole ne shi da dukkan magoya bayansa su mika wuya su karba kaddara Allah domin abubuwa suna faruwa ne kawai da yardarsa.
Ya ce a lokacin da gwamnatin sa ta hau mulki ya gana da dukkan manyan masu ruwa da tsaki a jihar kan yadda za su iya maido da dawwamammen zaman lafiya a jihar ta hanyar tattaunawar zaman lafiya inda ya ce har yau babu wani abu da ya fi Maida hankali akai kamar kawar da matsalar rashin tsaro a jihar.
Matawalle ya ce baya ga tattaunawar zaman lafiya da ‘yan fashin daji, ya kuma yi aiki tukuru don ganin cewa gwamnatinsa ta kawo ƙarshen bambamce-banbancen siyasa a jihar, ta hanyar haɗa manyan yan siyasar jihar wajen guda.