Karancin kuɗi: Gwamnan CBN ya nemi afuwar yan Nigeria

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emiefele, ya roki afuwar ƴan Najeriya kan matsalar da ake fuskanta wajen tura kuɗi ta intanet. Kwamitin tsare-tsare kan harkar kuɗi

Emefiele ya bayyana haka ne a taron kwamitin tsare-tsare kan harkokin kuɗi da aka gudanar a Abuja, inda ya tabbatar wa ƴan ƙasar cewa za a magance matsalar nan ba da jimawa ba.

A cewarsa, sashin da ke kula da biyan kuɗaɗe na babban bankin, ya yi iya kokarinsa don tabbatar da cewa an magance matsalar, a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fuskantar wahalhalu wajen aika kuɗi da wayoyinsu da kuma a na’urar cirar kuɗi ta POS.

An soma fuskantar matsalar ne tun bayan da gwamnati ta kaddamar da batun sake fasalta kuɗi wanda kuma ya janyo ƙarancin takardun kuɗi a faɗin ƙasar.

“Dole mu bai wa ƴa Najeriya hakuri. Mutane na cikin wahala kan rashin samun aika kuɗi ta intanet. Amma ina ganin ana kokarin shawo kan matsalar,” in ji Emiefiele.

A taron, gwamnan babban bankin ya kuma yi magana kan rashni wadatuwar takardun kuɗi a ƙasar saboda sake fasalin naira, inda ya ce bankin zai ci gaba da buga sabbin takardun kuɗi domin su wadatu musamman ma a kasuwanni

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...