Kwankwaso ya kokan kan jinkirta fadar sakamakon Zaɓen Kano

Date:

Daga Maryam Muhd Danali

 

Tsohon gwamnan jihar kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya koka tare da yin zargin ana Shirin kwace musu zabe.

 

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne ga yan jaridu a gidan sa dake Miller Road a Kano.

 

Yace suna Zargin ana Shirin yi musu abun da akai musu a zaɓen 2019 Inda aka ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, saboda wasu dalilai.

” To yanzu ma ga shi an lissafa kuri’un jam’iyyar mu ta NNPP ta ci zabe amma wai baturen zaɓen ya ki fadar sakamakon ya ma Kara lokacin, wannan Wani shiri suke yi na cutar da al’ummar jihar kano”. Inji Kwankwaso

 

Kwankwaso yace bisa alamu al’ummar jihar kano zasu wayi gari cikin bakin ciki saboda abun da hukumar zabe take shirin yi, wanda ya sabawa abun da mutanen kano suka zabe.

 

” Yanzu zaka gani gobe cewa zasu yi kowa kar ya fito saboda sun San abun da sukai Abu ne da bai kamata ba, ban taba ganin zabe irin wanann ba , mutane sun ce ga wanda suke so, Amma Yanzu suna shirin canja abun da aka zaba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...