2023: An harbe tsohon kansila kan zargin satar akwati a kano

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

Rahotanni na nuna cewa an harbe wani tsohon kansila a bisa zarginsa da sace akwatin kaɗa ƙuri’a.

Lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majaliasar dokokin jiha a ranar Asabar ɗin nan.

Rahotannin sun ce sojoji ne suka harbe Ibrahim Nakuzama, wanda tsohon kansila ne a mazaɓar Getso da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

Sai dai kawo yanzu rundunar sojan Najeriya ba ta kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba.

Wani makusancin mamacin ya ce tuni aka yi jana’izarsa a mahaifarsa a Getso.

Makusancin ya ce suna cikin jimamin rashin Ibrahim din, don haka babu wani bayani da zai ƙara.

Ibrahim Nakuzama ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa shida.

Ita ma a na ta ɓangaren, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane da dama saboda zargin tayar da hankali a lokacin zaben na ranar Asabar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...