Daga Rukayya Abdullahi Maida
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1000 za a ci gaba da amfani da su har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan kula da harkokin hulda da jama’a na bankin, Dakta lsa AbdulMumin ya fitar, Inda ya ce an cimma wannan matsayar ne a wani taro na kwamitin bankunan.
Ku Karanta: Sha’aban Sharaɗa ba takarar gaske yake ba, shi yasa na bar shi – Rarara
“A bisa bin ka’idoji da biyayya ga kotu, CBN a matsayin mai kula da bankunan kasuwanci, ta umarce su da su cigaba da karɓar da Kuma bada tsofaffin kudin kasar kamar yadda kamar yadda hukuncin kotun koli ya zartar wanda aka yanke a ranar 3 ga Maris”.
“Saboda haka, CBN ya gana da kwamitin ma’aikatan banki kuma ya ba da umarnin cewa tsofaffin takardun banki na N200, N500 da N1000 za a cigaba da amfani da su har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.
Makonni biyu da suka gabata ne dai kotun koli ta bada umarnin cigaba da amfani da tsofaffin kuɗin da CBN yace wa’adin su sun kare saboda an sauya fasalin wasu daga cikin kuɗaɗen Nigeria.
Da yake yanke hukunci a karar da jihohi uku suka shigar, kwamitin mutane bakwai na kotun koli ya bayyana cewa tsohon takardun kudi na N200, N500 da N1000 za a cigaba da amfani da su har zuwa karshen shekara.
(NAN)