Daga Rahama Umar Kwaru
Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami’antsa sun kama wani Basaraken gargajiya da tubabben ɗan Boko Haram da wasu mutum 35 bisa laifin safarar muggan ƙwayoyi.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta Twitter mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Femi Babafemi, ta ce ta samu nasarar kama muggan ƙayoyin a cikin na’urar daskarar da abubuwa ta ‘firinji’ da kuma tukwanen gas a filin jirgin sama na Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an hukumar sun kuma lalata gonakin da ake noma tabar wiwi da girmansu ya kai hekta 39.8 a jihohin Edo da Ondo.
Ban ce a zabi wani dan takarar gwamnan kano da ba Abba Gida-gida ba – Sen. Kawu Sumaila
Basaraken gargajiyar mai suna Baale Akinola Adebayo – sarkin Kajola, garin da ke kan iyakar jihohin Edo da Ondo – na daga cikin mutum 27 da hukumar ta ce ta kama da laifin safarar ƙwayoyin da nauyinsu ya kai tan 2.2 a faɗin jihohin ƙasar 12 cikin makon da ya gabata.
Haka kuma hukumar ta ce ta kama Alayi Modu – wanda ya ƙwashe shekara 15 yana cikin ƙungiyar Boko Haram – kafin ya miƙa wuya a shekarar 2021.
karanta: Ina da kyakyawar dangantaka da Shekarau, Kwankwaso da Ganduje – Gawuna
Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya jinjina wa jami’an hukumar a jihohin ƙasar 12 bisa namijin ƙoƙarin da ya ce sun yi wajen kamen miyagun ƙwayoyin.