Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Makarantar koyar da Tuki ta Dangote Articulated Truck Driving, ta yaye dalibai 50 da suka samu horo na musamman kan tukin manya motoci.
Makarantar tukin manyan motocin da ke Obajana a jihar Kogi ita ce makarantar koyar da tukin manyan motoci ta farko a Najeriya.
A shekarar da ta gabata ne tsohon shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) Dokta Boboye Olayemi Oyeyemi ya kaddamar da makarantar, wanda ya bayyana ta a matsayin wani gagarumin mataki na dakile matsalar hadarurrukan motoci da suka hada da manyan motoci a Najeriya.
Da yake jawabi a wajen bikin yaye daliban, Daraktan Sufuri (DDT), Mista Ajay Singh, ya ce sabbin daliban Kashi na 3 sun kammala karatun aji da aka kwashe watanni uku ana koya musu, yanzu kuma zasu je domin koyar abun da aka koya musu a aikace har na tsahon shekaru shida.
Tinubu zai gana da zaɓaɓɓun ‘yan majalisu kan shugabancin majalisun tarayya
Mista Singh ya ce makarantar ba wai kawai zata kawo raguwar haddura bane kawai, zata yi tasiri sosai ga Sauran masu ababen hawa da masu amfani da hanya.
A nasa bangaren, Manajan Makarantar Tuki da Motoci na Dangote Articulated Truck Driving School, Dangote Cement Transport (DCT) Obajana, Mista Daniel Marcus Akuso ya ce an gudanar da wannan gagarumin horon ne tare da hadin gwiwar FRSC da cibiyar horar da tuki ta Fantique na kasar Afrika ta Kudu.
A cewar Manajan makarantar, shirin horarwar na watanni uku ya taimaka wajen sauya yadda ake horar da direbobin.
Da yake jawabi, mataimakin kwamandan hanya, (OC Instructor) na hukumar FRSC mai kula da makarantar tuki ta Dangote, Engr Mukhtar Umar ya ce hukumarsa na taka rawar gani wajen horas da tsofaffin direbobi da sabbin wadanda aka horas da su.
“Muna koya musu yadda za suyi tuki cikin kwarewa, alamun hanya, nauyin direba, al’adar tuki, sannan mu ba su shaida,” in ji Engr Umar.
Babban sakataren hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE) Farfesa Idris Bugaje ya bayyana cewa NBTE na hada gwiwa da kamfanin Dangote wajen aiwatar da shirin makarantar.