Daga Aisha Aliyu Umar
Babbar kotun tarayya a Abuja ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta bayar da damar yin amfani da katin zaɓen wucin gadi a zaɓen ranar 18 ga watan Maris na gwamnoni da ƴan majalisar dokokin jihohi.
Alƙali Obiora Eguatu ne ya bayar da umarnin a lokacin da yake yanke hukunci kan ƙarar da wasu fusatattun ƴan Najeriya suka shigar ta neman a yi amfani da katin zaɓen wucin gadin a babban zaɓen a maimakon na din-din-din.
Alƙali Egwuatu ya ce an bayar da umarnin ne kasancewar masu shigar da ƙarar suna cikin kundin bayanan hukumar Inec.
Sai dai alƙalin ya ce bai amsa buƙatarsu ta uku ba da ke neman a bai wa kowane dan ƙasa da ke da katin zaɓen wucin gadi damar kaɗa ƙuri’a.
Da yake magana da ƴan jarida, lauyan masu ƙarar, mista Victor Opatola ya ce hukuncin nasara ce ga duka ƴan Najeriya da suka sha wahalar yin rajista amma suka rasa samun katin zaɓensu na din-din-din kafin lokacin zaɓen.