Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Babbar Mataimakiya ta musamman kan harkokin yada labaran na musamman Hajiya Zahrau Nasir Ahmad ta raba tallafin atamfofi ga mata sama 150 a unguwar sabuwar mandawari da shagari Quarters dake karamar hukumar kumbotso a jihar kano.
Da take bayyanawa wakilin Kadaura24 makasudin bada tallafin , Zahra’u Nasir tace ta bada tallafin ga matan duba irin muhimman cinsu a rayuwa da kuma dawai niyar da suke fama da ita a koda yaushe .

Tace a matsayin ta ta mai taimakawa gwamnan Ganduje wajibi ne agareta ta tallafawa Matan da suke tare da su, don duba da yadda gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta damu da al’amuran da suka shafi rayuwar mata da jihar kano baki daya.
- ” Gwamnan Kano ya dauki mata da matukar muhimmanci hakan yasa yake basu kulawa ta musamman don haka Akwai bukatar kuma ku Saka masa da abun alkhairi ta hanyar zaben Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo domin su dora akan aiyukan alkhairin da yake yiwa al’ummar jihar kano”. Inji Zara’u Nasir

Ta kara da shedawa matan cewa da zarar dan takarar gwamna na jam,iyyar APC DR Nasiru yusif Gawuna ya samu nasara zasu kara samarwa mata da matasa tallafi da jari domin su dogaro da kawunansu.
” Lokacin da na gayawa Dr. Nasiru Gawuna cewa zan baiwa matan unguwar mu tallafi , sai yace ki fada musu idan Allah ya tabbatar da mu a matsayin gwamnan Kano zamu yi ta baiwa mata da matasa tallafi har sai sun ce ya Isa , saboda yadda zamu baiwa harkokin mata kulawa ta musamman, kun ga Gawuna ya damu da ku don haka su zabe shi da mataimakin sa Murtala Sule Garo don ganin aiyukan alkhairi”. Inji SSA Special Broadcast

Daga karshe tayi Kira ga matan da sufito a ranar 18 ga watan maris domin zabar Dr. Nasiru yusif Gawuna da mataimakinsa murtala sulen garo da sauran yan takar karunsu na jam,iyar APC don ciga ba da yiwa jihar kano aiyukan alkhairi.