Ba a son rai na na kashe Ummita kuma ina roƙon kar a kashe ni – in ji ɗan China

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Wani dan kasar China mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47 a yau Alhamis ya sake fadawa wata babbar kotun Kano cewa bai taba niyyar kashe budurwarsa ‘yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani yar shekara 22, da aka fi sani da Ummita ba.

 

Wanda ake tuhumar wanda ke zaune a Railway Quarters Kano ana tuhumarsa da laifin kisan kai.

 

Da kauyan gwamnati, Musa Lawal ke tambayar dalilin da na zuwa gidan su Ummita ba tare da gayyata ba, kuma har ta aiko mishi da fefen bidiyon ta?, sai ɗan China ya kada baki ya ce shi bai yi niyyar kashe ta ba.

 

“Ban yi niyyar kashe Ummukulsum ba, kuma ba na son a kashe ni. Ta raunata ni a al’aurara kuma ba zan iya nunawa kotu cewa ya saba wa al’adun kasar Sin ba kuma ni musulmi ne.

 

“A wannan rana mai muni, sai ta kira na ta WhatsApp ta ce in kawo mata karen ta mai suna Charlie.

 

“Da isa ta gidan su, bayan ta ki daga waya ta, sai na aika mata da sakon tes, daga baya mahaifiyarta (Fatima Zubairu (Pw1)) ta bude gate, na shiga domin na dauko Charlie.

 

“Ban yi magana da mahaifiyar marigayiyar ba saboda ba ta jin Turanci kuma ni ba na jin yaren Hausa,” in ji Frank.

 

Haka dai aka riƙa titsiye ɗan China a kotun bayan kotun ta karɓi shaidun da aka kawo a kan kisan.

 

Daga nan sai mai Shari’aSanusi Ado Ma’aji ya dage ci gaba da shari’ar sai ranakun 29 da 30 ga watan Maris.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...