Mun haɗa tawagar lauyoyi 19 domin ƙalubalantar Nasarar Tinubu a Kotu – Atiku

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya haɗa tawagar manyan lauyoyi 19 domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka yi na ranar 25 ga watan Fabarairu.

 

Atiku ya yi wa lauyoyin bayani a yau Laraba a hedikwatar yaƙin neman zaɓensa a Abuja, inadl ya buƙace su da su tabbatar wa da kotu dokokin da aka keta a zaɓen tare da sake ƙwato abin da ya kira ikon ‘yan Najeriya.

 

Tawagar na ƙarƙashin jagorancin ƙwararren lauya mai zaman kansa JK Gadzama.

 

Ɗantakarar ya sheda musu cewa abu ne mai muhimmancin gaske su tabbatar sun tsaya tsayin daka domin tabbatar da nasara a shari’ar ba saboda shi ba kawai da PDP, domin ma sake tabbatar da dumukuraɗiyya domin ƴan gaba.

 

Tarin manyan lauyoyin sun haɗa da Chief Chris Uche da Paul Usoro da Tayo Jegede da Ken Mozia da Chief Mike Ozekhome da Mahmood Magaji da Joe Abraham da Chukwuma Umeh da Garba Tetengi da kuma Chief Emeka Etiaba.

 

Akwai kuma Chief Goddy Uche da Farfesa Maxwell Gidado da mai bayar da shawara kan shari’a na na ƙasa na PDP A.K. Ajibade da O.M. Atoyebi da Nella Rabana da Paul Ogbole da Nuremi Jimoh da kuma Abdul Ibrahim.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...