Rudunar ‘Yan sanda ta Kasa ta yi Nasarar Kama Mutane 203 a Zaben da ya Gabata

Date:

Daga Musa Mudi Dawakin Tofa

 

Rundunar ‘yan sanda ta Nigeria ta samu nasarar kama mutane 203 da take zarginsu da aikata laifuka daban-daban marasa dadin ji a lokutan zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisun wakilai na tarayya da ya gudanar a ranar Asabar 25/02/2023.

Kadaura24, ta ruwaito cewa Babban sufeton rundunar IGP Usman Alkali Baba ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar na kasa CSP Olumuyiwa Adejobi da aka aikewa kafafen yada labarai bayan gabatar wani taro na musamman da jami’an ‘yansanda na sassan daban-daban nan kasar nan, a ranar Litinin 06/02/2023 cikin babban dakin taro mai suna “Goodluck Jonathan Peacekeeping Hall” a helkwatar tsaro ta ‘yansandan kasar Nigeria dake babban birnin tarayya Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa taron ya mayar da hankali ne a kan bibiyar yadda aiyukan suka tsaro suka gudana a lokutan gudanar da zaben kamar yadda doka ta tsara tare da sake yin shiri don tinkarar zabe mai zuwa na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohin kasar, a ranar Asabar 11/03/2023.

Kazalika, a lokacin taron, Alkali Baba ya yabawa kokarin jami’an rundunarsa da sauran jami’an tsaro da suka nuna kwarewa da sanin makamar aiki wurin kama wasu ‘yansiyasa bata gari masu tada fitina da hargitsi a yayin gudanar da zaben da ya gabata.

IGP Usman Alkali Baba ya kara da cewa a lokutan zaben jami’ansu sun kai dauki da amsa kira zuwa muhimman warure 185 tare kama mutane 203 da kuma gano bindugu 18 boye a wasu wurare da ake zargi da tayar fitintuna da hargitsi a lokutan zaben, ya kuma ce za su cigaba da zurfafa bincike a kan duk wadanda ake zargi kana da zarar sun kammala, rundunar zata gurfanar da su a gaban shari’a don su girbi abin da suka aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...