Daga Safiyanu Dantala Jobawa
An rantsar da sababbin shugabanin kungiyar ma’aikata wanda ba sa shiga aji da dangoginta reshen ma’aikatar ilimi ta karamar hukumar Garun malam wato NASU.
Aisha Umar Alkali ce ta rantsar da su a matsayin wadan da za su jagoranci ‘ya’yan kungiyar ta NASU a karamar hukumar Garun malam. Bayan nan, ta gargade su da su kaucewa cin amana da rashin adalci a lokacin gudanar da shugabancinsu.
Haka zalika, Sakataren ilimi na karamar hukumar, Malam Sani Mato wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata, Yusif Dauda, ya ce “matukar suna bukatar ganin kungiyar ta samu cigaba to sai sun zama masu yin adalci tare da kaucewa son zuciya a tsakaninsu. Sannan ya yi musu fatan alheri.
Daga cikin wadan da aka rantsar din sun hadar da Ashiru Ayuba Yakasai Kura, a matsayin shugaba karo na biyu, da Hassan Abdu Garun malam a matsayin sakatare sai kuma Muhammad Saminu Kura a matsayin Ma’aji da dai saura mukamai daban-daban aka rantsar don tafiyar da kungiyar ta NASU dake karamar hukumar Garun malam.