Daga Rukayya Abdullahi Maida
A wani mataki na hana sauyin wurin aiki, CP Balarabe Sule, tsohon babban jami’in tsaron gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, zai koma Kano a matsayin kwamishinan ‘yan sanda.
Zai maye gurbin Mohammed Yakubu, wanda aka tura jihar makonni biyu da suka wuce.
Wata majiya daga cikin ‘yan sanda ta tabbatar wa DAILY NIGERIAN cewa babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali ya bayar da umarnin a tura jami’in dan sandan jihar kano.
Majiya mai tushe ta ce za a tura Balarabe Sule zuwa jihar Kano ne tare da ACP Abubakar Shika da ACP Adamu Babayo.
Balarabe Sule, wanda a kwanan nan aka kara masa mukamin ya koma kwamishinan ‘yan sanda, aka kuma tura shi jihar Cross Rivers , ya kasance mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka a Kano tsawon shekaru da dama.
Sakataren rundunar, DIG Hafiz Inuwa, wanda ya yada zango a Kano domin sanya idan a zaben jahohin Arewa maso Yamma bakwai, akwai yi yuwar a bashi umarnin komawa jihar Zamfara shi da jami’an sa.