2023: NNPP ta zargi gwamnatin kano da hayo ‘yan daba don kawo tsaiko a zaben gwamnoni

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

 

Jam’iyyar NNPP ta zargi gwamnatin jihar Kano da jam’iyyar APC a kano da shirye-shiryen yin magudin zabe , a zaΙ“en da za’a gudanar ranar Asabar 11 ga watan Marin din nan.

Tsohon dan takarar sanatan kano ta Arewa Dr. Abdullahi Baffa Bichi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a helkwatar jam’iyyar NNPP ta kano dake Sharada.
” Mun sami rahoton an kawo ‘yan daba daga jihohin kaduna bauchi da sauran jihohin Ζ™asar nan domin su tada hatsaniya a lokacin zaben gwamna da za’a gudanar a ranar asabar din nan, kuma an raba wadancan yan daba a dukkanin kananan hukumomin 44 dake jihar kano”. Inji Dr. Baffa Bichi
Dr. Baffa Bichi ya yi zargin cewa sun sami labarin gwamnatin jihar kano ta haΙ—a kai da wasu gurbatattun ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC reshen jihar kano domin yin magudin zabe ta hanyar jin kirta Kai kayan zabe da kuma tashi da wuri.
Ya kara da cewa suna yabawa kwamishinan ‘yan sandan jihar kano Saboda yadda yake gudanar da aikin sa cikin gaskiya da rikon amana, kuma yaki karbar duk wani tayi da gwamnatin ta yi masa don a hada kai da jami’in yan sanda a Kano.
” Tun da nake ganin zabe a Nigeria ban taba ganin zaben da aka sayi kuri’u kamar zaben da ya gabata ba, duk da cewa tsarin da babban bankin Nigeria ya fito na taΖ™aita zirga-zirga kudi, Amma duk da haka sai da suka sayi kuri’u da kayan abinchin da kayan sawa domin naga manyan motoci dauke da wadancan kayan, don haka muna kira ga daukacin hukumomin tsaro da masu yaki da cin hanci da rashawa da su sanya idanu a wannan zaben na ranar asabar”. Inji Dr. Baffa Bichi
Yayin zargin cewa ana yiwa ‘yan jam’iyyar NNPP da jagororin su barazana ta kamu da sauransu domin idan aka daure su baza a sake su ba har sai an yi zabe, kuma duk ana yi mana irin wannan ne saboda muna da son Zaman lafiya da kaucewa duk abun da zai haifar da rashin Zaman lafiya a kano.
Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari daΒ  hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su sani cewa baza su lamunci duk wani wulakanci a zaben gwamnoni da za a yi ranar Asabar ba, Inda ya kara dacewa basu da tabbacin zasu iya dakatar da Magoya bayan su idan aka yi musu abubun da basu dace ba .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related