Farfesa Gwarzo Ya Mika Sakon Ta’aziyyah Ga Hajiya Maryam Abacha Bisa Rasuwar Ɗanta

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

 

Wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer da Nijeriya, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Hajiya Maryam Abacha, matar Marigayi Janar Sani Abacha bisa rasuwar danta, Abdullahi Abacha.

 

Abdullahi Abacha, mai shekaru 36, shi ne na biyun karshe cikin ‘ya’yan Marigayi Sani Abacha, ya kuma rasu cikin kwanciyar hankali a barcinsa a gidan iyayensa da ke Abuja a ranar Asabar, 4 ga Maris, 2023.

 

Farfesa Gwarzo a cikin sakon ta’aziyyar da ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a Kano a ranar Asabar, ya bayyana rasuwar Abdullahi a matsayin mutuwa mai ban tsoro da damuwa.

 

Farfesa Gwarzo, wanda shi ne kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano, ya bayyana rasuwar Abdullahi Abacha a matsayin lamari mai tada hankali idan aka yi la’akari da yadda ya rasu yana matashi.

 

“A madadin iyalai, gamayyar Jami’ar MAAUN, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga mahaifiyarmu Hajiya Maryam Abacha da daukacin ‘yan’uwa bisa rasuwar Abdullahi.” Inji Farfesa Gwarzo a sakon ta’aziyyar.

 

Da yake jajantawa ‘yan’uwa da abokan arziki, Farfesa Gwarzo ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa dukkan kurakuransa, ya kuma saka sanya shi a Aljannar Firdausi.

 

Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya bai wa Hajiya Maryam Abacha da daukacin ‘yan’uwa ikon jure wannan babban rashi.

 

Tuni dai aka bizne Marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan da aka yi masa sallar jana’iza a babban masallacin kasa da ke Abuja a ranar Asabar.

 

Allah ya jikansa da Rahama ya sanya shi a Jannatul Firdaus, amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...