Lauyoyin mu sun shirya tunkarar Atiku da Obi a Kotu – Tinubu

Date:

Daga Kamal Umar Kurna

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya ce jam’iyyar ta shirya lauyoyinta tsaf waɗanda za su tunkari lauyoyin ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP da LP a kotu.

A ranar Alhamis ne Atiku Abubakar da Peter Obi suka ƙalubalanci sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Asabar ɗin da ta gabata suna cewa za su kai kotu, wanda ɗan takarar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a cikinsa , kuma INEC ta bayyan shi a matsayin wanda ya lashe shi.

Da yake tattunawa da manema labari daraktan hulɗa da jama’a kuma kakakin kwamitin Festus Keyamo, ya ce jam’iyyar ta tanadi tawagar manyan lauyoyi na Najeriya wanda suke a shirye domin kare nasarar da Tinubu ya samu lokacin da za su kotu da Atiku da Obi.

Ya ce “tuni mun haɗa tawagarmu ta lauyoyi. muna da waɗanda su kuma suka zo a raɗin kansu wanda dukkansu za su yi aikin kariyar.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...