Ji na ke kamar a aljanna na ke, in ji mutumin da ya auri mata 2 rigis

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Wani matashi mai suna Umar Sani da ya auri mata biyu a rana guda a garin Minna na jihar Neja ya ce ya na ji kamar ya na aljanna.

 

Sani, wanda ya auri Safina da Maryam a jiya Juma’a, ya shaida wa wata jarida ta yanar gizo da ke Minna, Tsalle Daya, cewa “Ina jin kamar an ba ni gida a aljanna, ina godiya ga Allah matuka, kuma farin cikinal da nake ciki ba zai musaltu ba.

 

“Na gode wa Allah da farin ciki na auri mata biyu a lokaci guda. Dukansu suna da fahimta, kuma ina godiya da hakan.

 

“Mutane da yawa sun yi tunanin cewa za a sami matsala daga ɗayar su, amma Allah cikin hikimarsa, ya sa abubuwa su ka kasance daidai.”

 

Umar ya bayyana cewa ya ya yi auren ne saboda shima da ga gidan mata sama da ɗaya ya fito.

 

“Tun ina dan shekara 10, na ga mahaifina yana da mata hudu kuma na ga yadda suke zaman lafiya. Na yi wa kaina alkawari zan auri mata fiye da daya idan na samu hali, ko in yi aure uku ko hudu a rana guda”.

 

Ko da yake ya ce iyayensa sun yi mamakin shawarar, amma ba su hana shi cika burinsa ba.

 

“Iyayena sun yi mamaki domin ko mahaifina bai auri mata biyu a rana daya ba. Amma ba su yi adawa da hakan ba. Abu mafi muhimmanci a gare mu a yanzu shi ne mu samu zaman lafiya,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...