Daga Nazifi Bala Dukawa
Zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Birni Engr. Sagir Ibrahim Koki ya jajantawa yan kasuwar Kurmi bisa iftila’in gobara da akayi a kasuwar, wanda yai sanadiyar konewar shaguna kusan guda dari.
Kasuwar kurmi kasuwa ce da ta shekara kimanin 600, ta sami gobara me a safiyar ranar Larabar da ta gaba ,inda aka sami asara mai tarin yawa.
Yayin da ya je kasuwar domin ganin irin asarar da sukai tare da jajanta musu bisa iftila’in, Engr. Sagir koki ya bukaci yan kasuwar da su dauki gobarar a matsayin kaddara daga Allah subhanallahu wata’ala.
Muna addu’ar Allah mayar muku da alheri ya kuma kiyaye gaba amin.
Sagir koki yayi wanan jawabi lokacin da yakai ziyarar jaje kasuwa harma ya tallafa musu da kudi naira dubu dari 200 domin rage musu radadi tare da yimusu Addu’ar Allah ya mayar musu da alkhari
Engr Sagir koki yayi Kira da gwamnati tarrayya data jihar kano data tallafawa Yan kasuwar dubada irin asarar da sukayi domin cigaba da sana’arsu
Anasa jawabin shugaban kungiyar Yan kasuwar bangaren masu sana’ar Leda alh danladi yayi godiya amadadin Yan kasuwar tare dayabawa Dan majalisar Kan kulawa da halin da suke ciki dayayi