Daga Maryam Abubakar Tukur
Wasu matasa karkashin kungiyar yan dangwale ta kasa reshen jihar Kano (Concern Nigerian Votes ) sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar asabar 25 ga watan fabarairun shekara ta 2023.
Maryam Abdullahi khalid da Ibrahim Muhammad sune wadanda suka yi magana a madadin ‘yan’yan Kungiyar na kasa reshen jihar Kano, sun ce sun shirya zanga-zangar lumanar ne don koken su ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.
Suka ce hukumar zaben ta gaza cika alkawuran da ta daukarwa yan Nigeria na gudanar da sahihi kuma karbabben zabe ga kowa ta hanyar yin amfani da wasu ka’idoji da ta kindayawa kanta.
” INEC ta yi alkawarin yin amfani da na’urar VBas, Amma mafi yawa a fadin Nigeria ba’a amfani da ita ba Kuma an yi zabe, sanann sun yi alkawarin sanya sakamakon zaben mazabu a Sashin su na yanar gizo Amma sun gaza yin hakan, don haka saboda wadannan dalilai muke kira da a soke zaben Shugaban kasa a kuma shirya wani sabo “. A cewar Maryam Abdullahi khalid
Shi kuwa Ibrahim Muhammad bukatar hukumar zabe ta kasa INEC yayi da ta dubi koken su ta hanyar soke zaben Shugaban kasa tare Kuma da shirya sabon Zaɓen, don cika alkawuran da shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmoud Yakubu ya yiwa yan Nigeria.