Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana nasarar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC ya samu a zaben shugaban kasa da aka kammala a matsayin Dimokaradiyya ta gaskiya.
Ganduje ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Malam Abba Anwar ya fitar a safiyar yau.
A cikin sanarwar, Anwar ya ce Gwamnan ya yaba da irin gwagwarmayar siyasa da jajircewar yan siyasar gidan Tinubu, wadda ta samar da nasarar sa a dukkanin fadin kasar nan, wajen tabbatar da cewa dan takarar shugaban kasa ya yi nasara a zaben da ya gudana.
“kudirin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi na gina dan Adam, ci gaban kasa da kuma dunkulewar kasa ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an so shi a dukkan sassan kasar nan,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Yakin da Tinubu ya kwashe shekaru da dama yana yi na kara tabbatar da mulkin dimokuradiyya a kasar, ‘yan Najeriya sun fahimce shi sosai. Don haka, muna ganin hikima da dalili mai inganci na mika masa makomarmu.”
Yayin da yake tabbatar da cewa, zababben shugaban kasar zai bullo da dabarun tunkarar matsalolin da suka addabi al’ummar kasar nan, Gwamna Ganduje ya yabawa shugabannin jam’iyyar APC da ‘ya’yan jam’iyyar “saboda tsayawa tsayin daka da suka yi har Tinubu ya sami nasara.
Gwamnan ya kara da cewa “Nasarar da Tinubu ya samu ba Najeriya kadai za ta amfana ba, za ta kasance wani kwarin gwiwa ga Afirka, a matsayinta na nahiya da kuma aiwatar da tsarin dimokuradiyya a duniya.”