Jam’iyyun PDP, da LP da kuma ADC sun bukaci da a sake gudanar da sabon zaɓe, suna masu cewa zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar, inda suka ce zaɓen na cike da kura-kurai.
Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu da sauran takwarorinsa na ADC Ralph Nwosu da Julius Abure na LP, sun bayyana haka ne a wani taron manema labarai da suka kira a Abuja yau Talata.
Jam’iyyun sun yi zargin cewa jami’an INEC sun tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar ta hanyar kin saka sakamakon zaɓen a shafin hukumar.
“Babu gaskiya a cikin wannan zaɓe, ana kuma ci gaba da soke sakamakon zaɓe a yankunan da jam’iyyun adawa ke da ƙarfi,” in ji Abure.
Sun kaɗa kuri’ar yankan kauna kan shugaban hukumar zaɓe farfesa Mahmood Yakubu, inda suka yi kira da ya gaggauta sauka domin wani ya maye gurbinsa da kuma gudanar da sabon zaɓe.
Jam’iyyun sun ce ba za su aminta da buƙatar saka sakamakon zaɓe a shafin hukumar zaɓe ba da shugabanta ya yi wanda kuma yake cikin sashi 60 na Dokar Zaɓe na 2022.