Kabiru Gaya ya Magantu, bayan bayyana sakamakon Zaɓen kano ta kudu

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Sanatan kano ta kudu Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana cewa ya karbi sakamakon zaɓen dan majalisar Dattawa na shiyyar Kano ta kudu da aka gudanar wanda ya bayyana Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP nasara.

Sanata Kabiru Gaya ya bayyana hakan ne cikin wani sakon murya da aka aikowa kadaura24 da yammacin ranar litinin din.
Kabiru Gaya ya kuma taya Kawu Sumaila Murnar lashe zaben, tare da bashi tabbacin ba zai ƙalubalanci sakamakon zaben a kotu ba.
” Sau hudu na ci zaben sanatan kano ta kudu Kuma a cikin hudun nan sau daya kawai aka taba kai ni kara kotu sauran 3 ba’a kaini ba, don haka ina sanar da kawu Sumaila cewa ba zan Kai shi Kara kotu ba Kuma ina taya shi murna”. Inji Sanata Kabiru Gaya
Sanata wanda yayi Sanatan kano ta kudu sau hudu ya godewa daukacin al’ummar yankin wadanda suka hadar da yan kasuwa Dattawa mata da matasa bisa hadin kan da suka bashi tsahon shekaru 16.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a safiyar Litinin din nan ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta aiyana Hon. Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP a matsayin sabon Sanatan kano ta kudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...