Za a rufe kasuwanni da kuma shaguna a gobe Asabar a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke shirin fita rumfunan zaɓe domin kaɗa kuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya.

‘Yan sanda sun bayar da sanarwar cewa za a takaita zirga-zirga a faɗin ƙasar a ranar Asabar har na tsawon sa’a 18, inda masu ayyuka na musamman kaɗai za a bari.

‘Yan Najeriya za su fita ne kawai zuwa rumfunan zaɓe, inda daga bisani bayan kaɗa kuri’a, za su koma gida.
A jihar Kano, mutane da dama na ta sayan kayan abinci gabanin zaɓukan ƙasar da aka daɗe ana jira saboda kasancewa babu zirga-zirga a ranar Asabar, inda ‘yan ake sa ran sai an sanar da sakamakon zaɓen kafin yawancin ‘yan kasuwa su koma wuraren kasuwancinsu.
Wani mai suna Shuaibu, ya faɗa wa BBC cewa zai saya wa iyalansa abincin da za su ɗauki tsawon kwanaki suna amfani da shi kamar yadda ya saba yi a zaɓukan baya.
“Kullum akwai rashin tabbas game da zaɓe a nan, don haka abu mafi kyau shi ne a shirya shi da isasshen abinci a gida,” in ji Shuaibu.
Ana sa ran zaɓen shugaban kasar da za a gudanar, zai kasance mai zafi wanda ba a gani cikin shekaru da dama.