Zaɓen 2023: Rundunar ‘yan sanda a Kano ta aiyana hana zirga-zirga daga 12 na dare yau

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano, ta ce ta hana zirga-zirgar ababen hawa a fadin Kano, daga karfe 12 na daren yau Juma’a zuwa karfe 6 na yammacin ranar Asabar (wato ranar zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisar tarayya).

 

Kakakin hukumar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka yayin wani atisaye da jami’an yan sanda suka gudanar yau a shalkwatar hukumar dake Bompai Kano, inda yace ba’a yarda wanda ba zaɓe zai yi yazo wajen zaɓe ba.

Talla

Kiyawa ya gargadi al’ummar jihar Kano, akan su bada hadin kai wajen gudanar da zaɓe cikin koshin lafiya, kada a dauki makami ko a sanya wani abu da yake nuna shaidar alamar wata siyasa.

Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil

Har ila yau, Kiyawa yace a sanya idanu da zarar an lura da wani motsi ko hanzari da ba’a yarda dashi ba, ayi ƙoƙarin sanar da jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...