Yanzu-Yanzu: Jam’iyyar PRP a madobi ta narke zata mara wa Musa Iliyasu Kwankwaso baya

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

Jam’iyyar PRP a karamar hukumar Madobi ta bayyana aniyar ta na marawa dan takarar majalisar tarayya na jam’iyyar APC a yankin kura madobi da garun Mallam Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso bayan a zaben da za’a gudanar gobe Asabar.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito wasu yan takarar majalisar tarayya na jam’iyyu guda uku a yankin kura madobi da garun Mallam sun hakura da takarsu tare da yin alkawarin yin duk mai yi yuwa don ganin Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi nasara a zaben gobe.
Talla
Shugaban kasa jam’iyyar PRP na karamar hukumar Madobi Hon. Ibrahim Isa Zanta madobi ne ya bayyana goyon bayan da PRP zata baiwa Musa Iliyasu Kwankwaso don ya zama dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam.
Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil
” Mu yan jam’iyyar PRP dukkanin mu zamu marawa Musa Iliyasu Kwankwaso na jam’iyyar APC bayan saboda dan garinmu ne, kuma yana da kwarewar da ya kamata mu mara masa bayan don cigaban kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam”. Inji Shugaban PRP.
Hon. Ibrahim Isa Zanta ya bada tabbacin zasu yi duk mai yiyuwa wajen ganin Musa Iliyasu ya sami nasara saboda zai kai musu cigaba yankin su, kuma zai yi musu kyakyawan wakilcin da basu taba samun irin sa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...