Daga Ahmadu Salisu Bachirawa
Sa’o’i kadan kafin fito kada kuri’a wasu yan takarar majalisar tarayya guda biyu a yankin kananan hukumomin Danbatta da Makoda sun narke tare da hakura da takarsu don marawa takarar Engr. Hamisu Ibrahim Chidari na jam’iyyar APC a zaben da za’a yi gobe Asabar .
Yan takarar wadanda suka hadar da na jam’iyyar ADP Mai suna Hon. Halilu Ado koguna da na jam’iyyar PRP Hon. Ibrahim Umar Ahmad sun ce sun ajiye takarar su ne saboda su mara baya ga dan takarar jam’iyyar APC Engr. Hamisu Ibrahim Chidari Shugaban majalisar dokokin jihar kano, don ya zama dan majalisar su, saboda suna da yaƙinin zai ciyar da yankin gaba .

Da suke bayyana janye takarar su a wannan dare yan takarar sun ce, sun ɗauki wannan matakin ne saboda chanchanta Engr. Chidari da kuma irin aiyukan cigaba da ya gudanar a yankin tun yana majalisar jihar, don haka suke da kyakyawan zato akan sa cewa zai ciyar da yankin gaba ta kowacce fuska.

” Mu da duk Magoya bayan mu, mun Amince zamu yi duk mai yiyuwa wajen ganin Hon. Speaker ya Sami nasara a zaben Ranar Asabar dake tafi don cigaban yankin kananan hukumomin mu na Danbatta da Makoda”. Inji yan takarar
Dukkanin yan takarar dai sun bada tabbacin zasu fito da duk magoya bayan su don su zabi jam’iyyar APC don Engr. Hamisu Ibrahim Chidari ya zama dan majalisar tarayya da zai wakilci kananan hukumomin Danbatta da Makoda .