Daga Rabi’u Usman
Kwanaki biyar da suka gabata muka tura Jami’an mu loko da Sako a fadin jihar nan domin samun Bayanan Sirri musamman a yayin zaben shekarar 2023 da za’a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.
Shugaban kwamatin kyautata Alaka tsakanin yan sanda da Jama’a (PCRC) dake kula da shiyya ta daya kano da jigawa (Zone 1) Comrade Ali Hassan T Bayero ne ya fadi hakan yayin ganawar sa da wakilin mu a wannan rana.

Yana mai cewa, ta haka ne za’a samu damar tsince bata garin da suke kokarin tashin hankalin jama’a yayin gudanar da zaben shekarar 2023.

Ya kara da cewar, sun samar da Wayoyin hannu na zamani da datar da za’ayi amfani da ita a yayin turo da sakonnin guraren da ake zargin mafakar bata garin ce a sassan kananan hukumomi 44 a nan kano.
Yana mai cewar, tuni Jami’an PCRC da aka tura su unguwannin suka fara turo da Bayanan, kuma an mika su ga babbar shalkwatar rundunar yan sandan kano domin fadada bincike.
Wakilin mu ya ruwaito cewa, daga nan yayi kira ga al’ummar jihar kano dasu bayyana dukkannin maboyar bata gari da aka sani a ko wacce unguwa a nan kano domin daukar matakin da ya dace.