Wasu ‘yan siyasa na shirin sayan kuri’a a zaɓen da ke tafe – EFCC

Date:

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya, Abdulrasheed Bawa, ya ce ‘yan siyasa na rike da sama da N500bn na tsofaffin kuɗi wanda ba a kai ga mayar wa Babban Bankin Ƙasar ba.

Abdulrasheed Bawa ya bayyana hakan ne a wani shiri na gidan talabijin na Channels na siyasar mu a yau.

Talla

Ya ce hukumar ta samu bayanai da ke nuna cewa ‘yan siyasa na shirin amfani da wasu hanyoyi na sayan kuri’a lokacin zaɓe.

Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil

“’Yan siyasa basu da wata mafita a yanzu illa ta sayan kuri’u saboda sun ga na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS za ta kawo musu cikas. Wannan bayanan sirri ne da muka samu. Sai dai, ina farin cikin cewa dukkan hukumomin tsaro na aiki tukuru wajen ganin an gudanar da zaɓen lami lafiya,” in ji Bawa.

Shugaban na EFCC ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su bai wa kungiyar haɗin-kai a ƙoƙarinta na yaki da masu sayan kuri’a a zaɓen Shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya da za a gudanar ranar Asabar.

Ya kuma buƙaci ‘yan ƙasar da su zaɓi mutane masu dattako da sanin ya kamata a zaɓen da ke tafe.

A cewarsa, sayan kuri’a babban batu ne da ke shafar makomar Najeriya da kuma ‘yan ƙasar, don haka ya kamata a dakatar da hakan ta kowace hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...