Daga Abdulrashid B Imam
Sanatan kano ta kudu Art Kabiru Ibrahim Gaya ya a bayyana cewa a matsayin sa na shugaban kwamitin harkokin zabe a zauren majalisar Dattawa ta kasa shi ne ya jagoranci yin dokar data magance magudin zabe a Nigeria.
Kadaura24 ta rawaito Sanata Kabiru Gaya ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a garin Sumaila lokacin da ya shiga garin domin bada tallafin jari ga matane 1000 a karamar hukumar.

Sanata Kabiru Gaya yace a wannan karon wadanda suka Saba satar akwatu a wajen zabe a wannan karon baza su iya yin hakan ba , saboda Sabbin dokokin da sukai wadanda suka magance yin magudin zabe.

” Idan mutum ya saba zuwa Wajen zabe ya saci akwatu to a wannan karon ba jar hula ba ko me ka Saka akan ka, zaka ka iya yin abun da ka saba ba, don haka ina baku tabbacin idan kuka sake zabe ne zan karasa muku aiyukan da an fara yi a Wannan karamar hukumar ta Sumaila”. Sanata Kabiru Gaya
Sanata Gaya ya kuma ce yanzu haka ya kashe Samar da naira Miliyan 500 domin samar da wani gidan ruwa a hayin gada wanda idan aka kammala shi , zai kawo ƙarshen duk wata matsalar ruwa a karamar hukumar Sumaila.
” Wadancan magudan kuɗade har Naira Miliyan dari biyar da na kashe Wajen gina rijiyoyin burtsatse da manyan tankuna da Kuma sola-sola da muka Saka , zan kara kashe naira Miliyan 150 domin kammala aikin, don haka ku zabi jam’iyyar APC a Rana ita yau domin na sami damar karasa muku aikin ta yadda ruwa zai shiga kowanne gida a karamar hukumar Sumaila “. A cewar Sanata Gaya