Daga Halima Musa Sabaru
Gabanin zaben 2023, biyar daga cikin jam’iyyun siyasa 18 a Nijeriya sun amince da mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar baya.
Jam’iyyun biyar sun bayyana hakan ne a babban taron gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a dandalin Mahmud Ribadu, da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa a yau Asabar.

Jam’iyyun dai sun hada da Allied Peoples Movement, African Democratic Congress, National Rescue Movement, Action Alliance da Action Peoples Party.

Shugaban gamayyar jam’iyyun, APM na kasa, Yusuf Dantalle, wanda ya yi magana a madadin jam’iyyun ne ya bayyana hakan.
A ranar Juma’a ne shugaban jam’iyyar APM na kasa ya amince da takarar Atiku a madadin ƴar takarar shugaban kasa mace daya tilo a jam’iyyar APM, a zaben shugaban kasa na 2023, Chichi Ojei.