Chanjin kudi: El-Rufai ya baiwa yan Kaduna Umarnin da ya sabawa na Buhari

Date:

 Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ƙalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari kan manufar sake fasalin naira, yana mai cewa tsofaffin takardun kudi za a ci gaba da karɓar su a jihar.
 A jawabinsa da ya yiwa al’ummar kasa da safiyar Alhamis, Buhari ya bayyana cewa an soke amfani da tsofaffin kuɗi na N500 da N1000 .
Talla
 Sai dai a jawabin da ya yi al’ummar a jihar Kaduna a daren ranar Alhamis, El-Rufai ya ce za a cigaba da amfani da tsofaffin kudin  har sai kotun kolin kasar nan ta yanke hukuncin akan haka.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
 “Don kaucewa shakku, duk tsofaffi da sababbin takardun kudi za a ci gaba da amfani da su a matsayin takardar kudi da doka aminta da su a jihar Kaduna har sai kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin akan batun.
 “Don haka ina kira ga daukacin mazauna jihar Kaduna da su ci gaba da yin amfani da tsofaffin da sabbin takardun kudin ba tare da wata fargaba ba. Gwamnatin jihar Kaduna da hukumominta za su rufe duk wani wurin da suka alki karbar tsofaffin takardun kudin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
 “Idan akwai bukata, za mu dauki wasu matakai masu tasiri kamar yadda doka ta tanada. Jawabin da shugaban kasar ya yi a safiyar yau ( Alhamis) da ya sanya dokar hana amfani da tsofaffin takardun kudi sai Naira 200 kacal, wanda ya nuna rashin mutuntawa da rashin biyayya ga hukuncin kotun koli na ranar 8 ga watan Fabrairu .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...