Ba za mu ɗauki malaman jami’ar da suke da ra’ayin siyasa aiki ba – INEC

Date:

Hukumar zaben Najeriya (INEC) ta ce ba za ta tura duk wani malamin jami’a da ke da alaka da wata siyasa aiki a zabukan kasar da za a fara nan da ‘yan kwanaki ba.

Sannan ta ce duk wani malamin jami’a da zai yi mata aikin wucin-gadi a zabukan kasar da ke tafe dole ne ya yi rantsuwar ‘yan ba-ruwanmu, wato ba ya wata jam’iyya ko siyasa ko goyon bayan wani dan takara.

Talla

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya sanar da haka jiya Alhamis a Abuja a lokacin wani taro da shugabannin jami’o’in kasar a Hukumar Jami’o’in Kasar (NUC).

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Sai dai ya ce daman ita rantsuwar ta tabbatar da cewa mutum ba shi da wata jam’iyya ko dan siyasa ko takara da yake goyon baya, tana hawa kan dukkanin ma’aikatan zabe ne kamar yadda sashe na 26 na dokar zabe ta 2022 ya tanada.

Jaridar daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban ya ce hukumar ba za ta tura duk wani malamin jami’a da ta san yana da alaka da wata jam’iyya ba.

“Haka suma wadanda watakila ba su shiga siyasa amma an san suna da dangantaka da wata siyasa ba za a dauke su ba. Hka suma wadnda aka yanke musu hukunci kan magudin zabe dole ne a ware su,” in ji shugaban na INEC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...