DA dumi-dumi: Kotun Koli Ta Dakatar Da Hana Amfani da Tsofaffin kuɗi

Date:

Daga Khalifa Abdullahi MaiKano

 A ranar Laraba ne kotun koli ta dakatar da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na dakatar da amfani da tsofaffin takardun kudi na naira daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2023.
 Wani kwamiti mai mutane bakwai karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro, ya dakatar da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka, a wani hukunci da ya yanke kan wata takardar kara da wasu jahohin Arewa uku da suka hada da Kaduna, Kogi da Zamfara suka gabatar.
 Jihohin ukun dai sun gabatar da bukatar a ba su umarni na wucin gadi na hana gwamnatin tarayya ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN) ko kuma bankunan kasuwanci dakatar da amfani da wasu daga cikin kudaden Nigeria a ranar 10 ga Fabrairu, 2023.
 Da yake gabatar da bukatar a ranar Laraba, lauyan wadanda suka shigar da kara, Mista A. I. Mustapha, SAN, ya bukaci kotun kolin ta amince da bukatar domin tabbatar da adalci da kuma jin dadin al’ummar Najeriya.
 Ya bayyana cewa manufar gwamnati ta haifar da “mummunan yanayi wanda kusan ke haifar da rikici a cikin ƙasar”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...