Bai kamata CBN ya sauya fasalin kuɗi a wannan gabar ba – Tinubu

Date:

Daga Auwalu Alhassan Kademi

 

Kwamitin Yaƙin neman Zaben dan takarar shugaban ƙasa na APC, PCC, ya ce bai kamata Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake tsara fasalin Naira a wannan lokacin ba.

 

Bayo Onanuga, Daraktan watsa labarai da wayar da kan jama’a na kwamitin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a a Abuja.

 

“Manufar sake fasalin naira ta zama wani nauyi da ‘yan Najeriya ba za su iya dauka ba,” in ji Onanuga, inda ya kara da cewa ‘yan Najeriya da dama na shan wahala wajen karbar kudadensu daga asusun su saboda manufar.

Talla

Ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan adawa da kiran da CBN ya yi na kara wa’adin musanyar kudin naira a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

“Yin zagon kasa da canjin kudi na Naira da karancin man fetur a sassan kasar nan ya janyo wa miliyoyin ‘yan Najeriya wahala.

 

“Ci gaban ya bayyana hakikanin halin PDP da Atiku a matsayin makiyin jama’a lamba daya.

 

“Tun da CBN ya gabatar da manufofin musanya kudi da kuma sabbin tsare-tsare na Naira, Atiku Abubakar da PDP sun yi shiru na mugunta.

 

Onanuga ya ce, “hakan ya nuna cewa su na amfana da rashin jin dadin manufofin da za su haifar wa ‘yan Najeriya da kuma bacin ran da zai haifar wa APC,” in ji Onanuga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...