Ba za mu kara wa’adin Chanjin kuɗi daga 10 ga Fabrairu ba, Emefiele ya gargadi ‘yan Najeriya

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

 

Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ba ya tunanin kara tsawaita wa’adin karɓar tsoffin kudaden da aka sauya musu fasali ba.

 

 

‘Yan Najeriya ciki har da gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC, sun bukaci babban bankin kasar da ya kara tsawaita wa’adin, sakamakon karancin kudin da aka yi wa kwaskwarima a cikin al’umma.

Talla

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Sai dai gwamnan babban bankin na CBN, Godwin Emefiele, ya ce bankin ba ya tunanin tsawaita wa’adin bayan wa’adin kwanaki 10 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi kwanan nan.

 

 

Emefiele, wanda ya bayyana hakan a wani taron karawa juna sani da aka yi a Legas, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri ganin cewa nasarorin da aka samu a manufofin sun fi kalubalen yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...