Kotu ta Aike da Shahararriyar ‘Yar TikTok Murja Kunya Zuwa Gidan Yari

Date:

Daga Nazifi Bala Dukawa

 

Babbar kotun shari’ar musulunci dake filin hokey ta aike da murja Ibrahim kunya zuwa gidan gyaran Hali.

 

Kadaura24 ta rawaito an gurfanar da ita a gaban kotun inda aka zargeta da laifukan bata suna, tayar da hankali da kalaman batsa da barazana.

 

Lauya mai gabatar da Kara lamido Abba soron dinki shi ne ya karanta mata kunshin tuhume-tuhumen da ake yi mata, Inda nan take ta musanta zargin.

 

Lauyan Murja Ibrahim Kunya Barr. Yasir Umar Musa ya nemi da a sanyata a hannun belli .

Talla

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Alkalin babbar kotun shari’ar musuluncin dake zaman ta a filin hocky Mai Sharia Abdullahi halluru abubakar ya yi umarni da kai Murja zuwa gidan yari, sannan yace a mai da ita gaban kotu ranar 16 ga wata domin bayyana matsayar kotu Kan Neman bellin.

 

Lauyan Murja kunya ya nemi da’a kaita hisbah kafin waccan rana domin dai yimata wa’azi da nasiha kan zargin da akai mata.

 

A bakon da ya gabata ne Kadaura24 ta rawaito cewa rundunar yan sandan jihar kano ta kama Murja Ibrahim Kunya wacce ta shahara wajen yin kalaman batsa da zage-zage a dandalin sada zumunta na TikTok.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...