Da Dumi-Dumi: CBN Ya Umarci Bankuna Su Fara Biyan Sabbin Akan Kanta

Date:

Daga Ali Abdullahi Fagge

 

 

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan da su fara biyan biya mutane da Sabbin kudaden Naira a kan kanta (cikin banki), Amma kar ya Kai sama da Naira dubu 20,000 a kowace rana.

 

 

Kadaura24 ta rawaito Daraktan Sadarwa na Bankin, Osita Nwanisobi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa babban bankin zai hada gwiwa da hukumar ‘yan sandan Najeriya, hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS), hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da kuma sashin kula da harkokin kudi na Najeriya (NFIU). ) don hukunta masu wulakantawa da sayar da sabbin kudaden.

 

 

Ya ce: “Babban Bankin Najeriya (CBN) ya lura, tare da nuna matukar damuwa, kan yadda wasu mutanen suke siyar da sabbin takardun kudi da aka yi wa kwaskwarima da kuma wadanda ke yin abubuwan da basu dace ba da kuɗin, ta hanyar yin liki a wuraren bukukuwa, wanda hakan ya sabawa doka.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Talla

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Umarnin farko dai da babban bankin ya bayar ita ce kada kowanne banki ya bada sabbin kudaden a Cikin banki sai dai a injin ATM.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...