Yanzu-yanzu: Bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe har bayan ƙarewar wa’adi – CBN

Date:

Daga Kamal Umar Kurna

 

Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, CBN, Godwin Emefiele, ya ce bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi na Naira har bayan wa’adin musanya wa da sabbin kudi ranar 10 ga Febrairu.

 

A ranar Lahadi ne babban bankin ya kara wa’adin rufe karɓar tsoffin takardun Naira na 1,000 da 500 da kuma N200, biyo bayan korafin ‘yan Najeriya.

Talla

Sai dai a yayin da Emefiele ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan sabon tsarin sauya fasalin Naira ,da kuma canjin naira a yau Talata, shugaban na CBN ya ce har yanzu bankuna za su karbi tsoffin takardun har bayan wa’adin.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Emefiele ya ce idan aka yi la’akari da sashe na 20, karamin sashe na 3 na dokar CBN ta 2007, ko da wa’adin amfanin tsoffin kuɗaɗe ya cika, CBN za ta ci gaba da karbar su.

 

Emefiele ya ce dole ne bankunan kasuwanci su karbi kudin ko da bayan wa’adin 10 ga watan Fabrairu ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...