Da dumi-dumi: Buhari ya Bude Tashar Tsandauri ta Dala a Kano

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso jihar kano domin bude wasu muhimman aiyuka da gwamnatin tarayya da ta Kano suka gudanar.

Kadaura24 ta rawaito Shugaba Buharin ya isa tashar tsandauri ta Dala dake Zawaciki a karamar hukumar kumbotso ta Kano da misali karfe goma da mintina 23.
Talla
Shugaba Buharin ya Sami tarba daga Gwamna jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da masu martaba sarakunan Bichi Rano Gaya da Karaye da sauran ministoci da kwamishinoni gwamnatin kano.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Y kaddamar da tashar wadda zata baiwa yan kasuwa damar kawo kayan su daga ko Ina a duniya, maimakon yadda a baya sai sun je jihar Legos sun dauko, wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin jihar kano da kasa baki daya.
Yanzu haka Shugaban Kasar da Gwamna Ganduje sun tafi garin Tiga domin bude gidan wuta, wanda gwamnatin jiha kano ta samar daga nan zai je gidan sarki da sauran wuraren da zai ziyarta ta a yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...