Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta Musamman da Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a gidan sa dake Daura.
Kadaura24 ta rawaito Cikin wasu hutuna da Babban mataimakin na musamman ga gwamnan kano kan harkokin hotuna Aminu Dahiru ya fitar a yammacin wannan rana ta lahadi sun nuna yadda Shugaba Buhari da Ganduje suka yi ganawar sirri.

Ana dai hasashen ganawar ta su baza rasa nasaba sa da zuwan da shugaban kasa Buhari zai yi kano a gobe Litinin ba.

Daga cikin wadanda Ganduje ya je da su gidan Buhari akwai Shugaban masu rijaye na majalisar wakilai Hon. Alhassan Ado Doguwa da shugaban majalisar dokokin jihar kano Hon. Hamisu Ibrahim Chidari da sanata Barau Jibril da Sanata Kabiru Gaya.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta gwamnatin jiha kano ta rubutawa fadar shugaban kasa wasikar bada shawarar dakatar da ziyarar Shugaba Buharin zuwa kano saboda wasu dalilai.
Zamu cigaba da bibiya don kawo muku yadda ta kasance.