Shugaba Buhari zai zo Kano gobe don bude ayyuka guda 8

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari da zai zo ziyarar aiki domin kaddamar da wasu ayyukan raya kasa guda takwas a jihar.

 

Kadaura24 ta rawaito Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba ya fitar ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai karbi bakuncin shugaban kasar da shi da mukarrabansa.

Talla

 

Ya ce idan ya zo Kanon, Buhari zai kaddamar da gidan wuta na kano mai karfin megawatt 10, da Dala Inland Dry Port dake a Zawachiki, karamar hukumar Kumbotso.

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Sauran aiyukan da zai bude sune hukumar adana bayanai ta jihar Kano da ke Audu Bako Secretariat, kamfanin Galaxy Backbone Limited Project da ke titin Ahmadu Bello Way.

 

 

Sauran sun hada da cibiyar kula da Masu cutar daji a asibitin kwararru na Muhammadu Buhari, Giginyu; Gadar Muhammadu Buhari dake NNPC, kan titin Maiduguri; cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote Ultra-Modern Skill Acquisition Centre, Zaria Road da Rukunin Gidajen Gwamnatin Tarayya dake Gandun Sarki, Darmanawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...