Daga Shehu Sulaiman Sharfadi
Shugabancin kungiyar kasuwar abinci ta duniya dake Dawanau a karamar hukumar dawakin tofa ta bayyana gamsuwar ta dangane da Karin kwanaki goma da babban bankin kasar nan yayi domin mayar da tsoffin kudade bankuna don kada kananan yan kasuwa su tafka asara.
Sakataran kungiyar wanda kuma Garkuwan matasan Arewacin Nigeria, Kwamared Rabiu Abubakar tumfafi ne ya sanar da hakan a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.

Garkuwan ya godewa Allah tare da babban bankin kasa, bisa wannan dama da ya baiwa yan kasuwa musamman kananan wadanda basu da asusun Ajiyar banki domin su samu damar shigar da kudadensu bankuna kafin wa’adin ya kare domin gudun tafka asara.

Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya da babban bankin kasar nan bisa yin wannan hange da suka yi wajen Karin wa’adin, wanda ba don haka ba da wannan tsarin na baya ya karya yan kasuwa da dama musamman kananan yan kasuwa tare da durkushewar kasuwanci da tattalin arziki a fadin kasar nan.
Don haka yake kira ga ‘yan kungiyarsu na birni da na karkara da su tabbata sun yi amfani da wannan karin wa’adin da babban bankin kasar nan ya yi wajen mayar da tsoffin kudadensu bankuna kafin wa’adin ya kare domin gudun tafka asara.
Kwamared Rabiu Abubakar tumfafi ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da babban bankin kasar nan kan ya yi kokari wajen ninka kudaden da yake turawa kananan bankunan, domin Kudaden su yawaita a hannun al’umma, wanda ko da wa’adin da babban bankin kasa ya kara bazai illata al’umma da kananan yan kasuwa ba.
Daga nan sai ya yi kira ga matasan jihar kano da su kaucewa aibata shugabanni ko furta kalaman batanci musamman ma kan ziyarar da Shugaban kasa Muhammad Buhari zai kawo jihar Kano.
Don haka ya shawarcesu d su fito su tarbi Shugaban kasa cikin lumana ba tare da tashin hankali ko tada tarzoma Ba.