Daga Ali Abdullahi Fagge
A karshe dai babban bankin Najeriya CBN ya kara wa’adin daina karɓar tsofaffin kudi har zuwa nan da kwanaki 10.
Kadaura24 ta rawaito a wata sanarwa da gwamnan babban bankin na CBN, Godwin Emefiele ya fitar a ranar Lahadi, ya ce sabon wa’adin zai kare ne 10 ga watan Fabrairun 2023.

Duk da haka, har yanzu ’yan Najeriya za su iya mika tsofaffin takardun Kudinsu kai tsaye zuwa bankin CBN har nan da ranar 17 ga Fabrairu, 2023.

‘Yan Najeriya dai sun yi ta kokawa kan rashin wadatattun sabbin kudin wanda da farko aka ce wa’adin zai kare a ranar 31 ga watan Janairu .
A baya dai CBN ta ce ba za ta kara wa’adin ba.