Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Duk da karancin kudin da aka sauyawa fasali a cikin kasuwanni da hannun al’umma, yanzu haka an hangi wasu mutane sun dira filin ajiye motoci na Dadi da ke Sabon Gari-Zariya a Jihar Kaduna Inda suke sayar da kudaden a kan farashi mai tsada.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ga manyan layukan da ke kunshe da nau’o’i daban-daban na takardun kudaden da aka baje kolinsu a kofar tashar mota ta Dadi, unguwar Kwangila a cikin birnin Zariya don masu so su saya.


Wani bincike da NAN ta yi ya nuna cewa ana sayar da damin Naira 200 akan N30,000, takardun N500 akan N70,000 sannan ana siyar da N1,000 akan N130,000.
Wani dan kasuwa mai suna Mohammed Bello, ya ce sun biya tsakanin N70,000 zuwa N130,000 don samun sabbin takardun kudi na N500,000.
Duk da dokar da ta haramta safarar kudaden Naira da tsabar kudi, wadanda suka aikata wannan aika-aika suna gudanar da sana’o’insu cikin walwala a kusa da ofishin ‘yan sanda a Kwangila, Sabon Gari Zariya.
Da Majiyar Kadaura24 ta tuntubi , DSP Mohammed Jalige, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ya bayar da tabbacin cewa ‘yan sandan za su kara kaimi wajen dakile wannan aika-aika.