An bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya duba irin wahalar da talakawan kasar nan suke ciki kan canza fasalin kudaden kasar na 200 da 500 da 1,000.
Kadaura24 ta rawaito Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta kasa ita ce tayi wannan Kiran a wata sanarwa mai dauke dasa hannun Sakataren Kungiyar na kasa Shehu Tasi’u Ishaq.
Sanarwar tace bisa la’akari da kuracewar wa’adin da Babban bakin kasa ya bayar na daina amfani da kudaden da aka sauya musu fasali ya janyo shiga halin kakanikayi ga talakawan kasar nan.
Kazalika al’uma sun shiga halin matsi da yunwa da fatara wanda hakan ka iya haifar da mummunar rayuwa ga alumar kasar nan.

A Don hakane kungiyar Samarin Tijjaniyar tayi kira da babbar murya ga shugaba Buhari ya duba wannan hali da al’umar kasar nan ke ciki, kuma ya tuna cewa talakawa ne suka tsaya tsayin daka wajan tabbatar dashi a matsayin da yake akai.

Daga nan sai Kungiyar ta bukaci shugaba Buhari da ya umarci babban Bankin kasa wato Centarl Bank ya Kara wa’adin yin amfani da tsofaffin kudaden domin al’uma su samu damar shigar da wadanda suke hannunsu a bankuna
Haka kuma sanarwar ta bukaci al’umar wannan kasa su kwantar da hankulansu tareda cigaba dayin addu’ar samun sassauci a cikin wannan lamari domin samun ingantacciyar rayuwa.